Tsohon shugaban Hukumar EFCC, Nuhu Ribadu ya bayyana wa dubban magoya bayan sa a garin Yola cewa lallai shugaba Muhammadu Buhari ya cancanci zarcewa a 2019 domin ci gaba da ayyukan ci gaba da yake yi a kasar nan. Ribadu ya ci gaba da cewa da ga wannan rana ta Litini, ya mika wa Kamfen din Buhari gaba daya motoci, ofisoshi da kayayan aiki da yayi amfani da su a wajrn neman takarar gwamnan jihar Adamawa da yayi. Bayan haka ya zano wasu dalilai da ya ce hujjojine ga duk mai kaunar Buhari da ma ‘Yan Najeriya su sake zaban sa a karo na biyu musamman ga mutanen yankin Arewa maso Gabas. 1 – zaben 2019, zabe ne da zai banbanta tsakuwa da aya. Zaben kauce wa irin fuskokin da suka rugurguza kasar nan a rungumi gwamnati mai adalci. 2 – Inganta wa da samar da tsaro mai nagarta kamar yadda ake dandanawa yanzu musamman a jihar Adamawa. 3 – Ayyukan ci gaba da ake samu a karkashin wannan gwamnati musamman a sassab jihar da ba ataba samun irin haka nuni ne cewa wannan gwamnati da take da mu...