AZ:5700/KS/PRD/VOL.3/82 31st/12/2018
Rundunar Yan Sanda ta Kasa, Reshen Jihar Kano, Karkashin Jagorancin Kwamishinan Yansanda CP Rabi’u Yusuf psc+ ta Samu Nasarori da dama a Shekarar 2018, da muke bankwana da ita, a Yunkurinta na kare rayuka da dukiyoyin Al,umma da kuma inganta sha’anin tsaro a Jihar Kano.
Alkaluma Sun nuna cewa an samu Nasaroro da dama ta fannin laifukan da suka shafi fashi da makakami, da masu garkuwa da Mutane da Masu fyade, da kisan kai da kwacen motoci. A yunkurinta na ganin an samu ingantattun harkokin Siyasa da Zabubbuka ba tare da rikice-rikece ba, rundunar yan sandan Jihar Kano ta shirya tarukan wayar da kan Masu ruwa da tsaki muhimmancin zaman lafiya a yayin Zabe. An samu raguwar ayyukan batagari a 2018 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata. A Shekar da ta gabata an samu laifuka 337, Wanda suka hadar da Fashi da makami 22, Garkuwa da Mutane 21, laifukan fyade 105, kisan kai 168,Satar Motoci 34, da sauransu.
Rundunar ta kuma kama Yan Daba 2487. An samu kwato Bindigogi , wadanda suka kunshi kirar gida dana kasashen waje. An samu harsashi masu rai 269. Baki daya an samu raguwar laifuka da aka samu idan ida aka kwatanta da Shekara 2017.
Alkaluman da aka samu, sun nuna cewa an samu raguwar aikata laifuka a Jihar. Rundunar Yansandan Jihar Kano na mika godiya ga Gwamnatin Jihar kano da Masarautar Kano da al’ummar Jihar Kano, da Kungiyoyin da ba na Gwamnati ba da sauran Hukumomin Tsaro da kafafen yada labarai.
Rundunar Yansandan Jihar kano karkashin jagorancin Kwamishinan Yansanda CP Rabiu Yusuf psc+ na taya al’ummar Jihar murnan Sabuwar Shekara, tare da fatan ci gaba da samun zaman lafiya da kwanciyar Hankali da lumana da karuwar Arziki a Jihar Kano.
SP. MAGAJI MUSA MAJIA,
POLICE PUBLIC RELATIONS OFFICER,
FOR: COMMISSIONER OF POLICE,
KANO STATE.
Comments
Post a Comment