Jami’an hukumar yan sandan Najeriya sun damke wasu yan fashi da garkuwa da mutane da suka addabi jihar Zamfara, arewa maso yammacin Najeriya. Wadannan yan ta’addan ne suka sace wasu yan mata yan biyu kwanakin baya. Babban jami’in hukumar yan sanda, DCP Abba Kyari ya bayyana hakan ne a ranan Litinin, 31 ga watan Disamba, 2018 a shafinsa ta Facebook inda ya jero sunayensu:
i. Nafiu Usman 28yrs a.k.a Baba Doctor, native of Wanke village in Gusau LGA – Sectional Leader
ii. Ma’aruf Usman of Wanari Village in Zurmi LGA
iii. Inusa Usman 40yrs native of Zurmi LGA
iv. Awal Jibril 41yrs native of Mada LGA
v. Shehu Mohammed 55yrs
vi. Alhaji Ibrahim Ibrahim 35yrs
vii. Ibrahim Sani 45yrs
viii. Kabiru Usman 30yrs
ix. Bala Garba 60yrs
x. Maigari Labbo 56yrs
xi. Mohammed Abdullahi Aramako 31yrs
xii. Salisu Mamman Wadatau 38yrs of Danjibga LGA
Idan za’a tuna a ranar 25 ga watan Oktoba ne aka samu rahoton sace yan matan da wata gungun masu garkuwa da mutane suka yi a lokacin da suke kan hanyar raba ma yan uwansu da kawayensu ankon bikinsu wanda ake gab da gudanar da bikin. An sace yan matan ne a karamar hukumar Zurmi ta jahar Zamfara, kamar yadda mataimakin shugaban hukumar Abubakar Muhammad ya bayyana, inda yace an sace mutane bakwai a cikin kwanaki biyu, daga cikinsu har da tagwayen. Daga baya suka bayyana cewa zasu kashe tagwayen matukar ba’a biya musu bukatarsu na biyan kudin fansa ba. Ba da dadewa ba aka sako yan matan bayan gudunmuwar da wasu yan siyasan jihar suka taimaka da kudin fansar 15m.
Comments
Post a Comment