Rundinar Yan Sanda Nigeria Sun Samu Nasaran Kama Wadanda Sunkayi Garkuw Da Yan Mata Tagwaye A Jihar Zamfara
Daga Datti Assalafiy
Rundinar 'yan sandan Nigeria sun samu nasaran kama rikakkun barayi masu sace mutane wadanda sukayi garkuwa da 'yan mata 'yan tagwaye Hassana Bala da Hussaina Bala 'yan shekaru 18 a jihar Zamfara watanni biyu da suka gabata
Idan ba'a manta ba a ranar 21-10-2018 ne akayi garkuwa da 'yan tagwayen a kauyen Dauran karamar hukumar Zurmi jihar Zamfara lokacin da sukaje garin mahaifinsu zasu raba katin aurensu, wadanda sukayi garkuwa dasu basu sakesu ba har sai da aka biyasu kudin fansa naira miliyon goma sha biyar (N15,000,000)
Tun daga lokacin da akayi garkuwa da 'yan matan rundinar 'yan sanda take bin diddigin lamarin, kuma an samu nasaran cafke wadanda sukayi garkuwa dasu a maboyarsu dake jihohin Zamfara da Katsina, kuma sun amince da aikata laifin tare da sauran miyagun laifuka da suka aikata, sannan sunce sun kasafta kudin fansa da suka karba naira miliyon goma sha biyar (N15,000,000) sun raba kowanne ya samu kasanso naira dubu dari biyar (N500,000)
Ga sunayensu kamar haka:
1-Nafiu Usman 'dan shekara 28 wanda yafi shahara da sunan (Baba Doctor), ya fito daga kauyen Wanke karamar hukumar Gusau jihar Zamfara, kuma shine shugaban masu garkuwan.
2- Ma'aruf Usman daga kauyen Wanari karamar hukumar Zurmi jihar Zamfara.
3- Inusa Usman 'dan shekara 40 daga karamar hukumar Zurmi LGA.
4- Auwal Jibril 'dan shekara 41 daga karamar hukumar Mada .
5- Shehu Mohammed 'dan shekara 55.
6- Alhaji Ibrahim Ibrahim 'dan shekara 35.
7- Ibrahim Sani 'dan shekara 45.
8- Kabiru Usman 'dan shekara 30.
9-Bala Garba 'dan shekara 60.
10- Maigari Labbo 'dan shekara 56.
11- Mohammed Abdullahi Aramako dan shekara 31.
12- Salisu Mamman Wadatau 'dan shekara 38 shine babban mai bayar da bayanan sirri ga masu garkuwan.

An samu bindigogi kirar AK47 guda shida (6) a tare dasu, sannan magazin guda hudu (4) da harsashin bindiga guda talatin da hudu (34) da adduna guda hudu (4), da zaran an kammala bincike za'a mikasu zuwa kotu don fuskantar hukunci.
A gaskiya wadannan barayin sun tayar mana da hankali sosai, kuma sun wahalar damu, yanzu kuma zasu fuskanci mummunan sakamakon abinda suka aikata tun daga nan duniya.
Allah ka taimaki jami'an tsaron mu, ka kara musu taimako da nasara Amin.
Comments
Post a Comment