Rundinar sojin Nigeria ta fitar da sanarwa yanzunnan daga kakakin rundinar Birgediya Janar Sani Usman Kuka Sheka cewa dukkan yunkurin da wasu gurbatattun mutane sukeyi wajen kawo cikas game da yaki da ayyukan ta’addanci da ‘yan bindiga a Nigeria ba za’a lamunta ba
Rundinar sojin Nigeria ta lura da cewa akwai wasu gurbatattun mutane da gurbatattun ‘yan siyasa da suke kokarin siyasantar da lamarin yaki da ayyukan ta’addanci a fadin tarayyar Nigeria a halin da ake ciki yanzu
Wannan lamari ya faru ne sakamakon fitar da tsoffin faifan videon farfaganda na ‘yan ta’addan Boko Haram da wasu keyi, da fitar da tsoffin audio na wasu matsoratan sojojin da suke hira da ‘yan jarida, da fitar da rahoton karya wanda wasu kebantattun kafofin watsa labarai makiya zaman lafiyar Nigeria keyi
Har ila yau; rundinar sojin Nigeria ta lura da cewa akwai wasu gurbatattun mutane ‘yan siyasa da suke kokarin yin batanci ga gwamnati akan kokarin da gwamnatin takeyi wajen tabbatar da tsaro da kare rayukan ‘yan Nigeria, babban ajandarsu shine su sanyaya gwiwar dakarun sojoji da suke fagen daga a arewa maso gabashin Nigeria, ta yanda dakarun zasu karaya game da yakin da sukeyi, wanda hakan zaisa gurbatattun ‘yan siyasar su cimma mummunan burinsu
Don haka rundinar sojin Nigeria tana jaddada wannan bayanin, domin kowa ya san da cewa Nigeria tana yaki da ‘yan ta’addan Boko Haram ne ta dukkan salon da zasu bayyana ko suka bayyana, don haka rundinar sojin tana gargadin duk masu yin amfani da yakin da take da Boko Haram wajen cimma mummunan burinsu da su shiga taitayinsu, domin rundinar ba zata kyale duk wani yunkuri na sanyaya gwiwar mayakanta ba, wanda karshe zaisa mayakan su gudu daga bakin daga
Rundinar sojin Nigeria zata cigaba da sa ido akan dukkan farfagandar da gurbatattun mutane suke yadawa tare da daukar matakin gaggawa da ya dace a kan irin wadannan mutane, rundiar sojin Nigeria zata cigaba da gabatar da zazzafan yaki akan ko wani irin nau’i na ayyukan ta’addanci da tsageru ‘yan bindiga a Nigeria ba tare da jin shakkar kowa ba.
Rundinar sojin tana rokon jama’a da su yada wannan sanarwan a dukkan kafofinsu na watsa labarai, sanarwan ya fito daga kakakin rundinar sojin Nigeria Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka.
Muna rokon Allah Ya taimaki sojojin Nigeria Ya basu sa’a da nasara akan ‘yan ta’adda da masu tallafa musu ta kowace fuska.
Comments
Post a Comment