Rahotanni daga kafafen yada labaran Amurka sun ce an kashe Hamza Bin Laden, dan tsohon shugaban kungiyar Al-ka’ida marigayi Osama Bin Laden. Har yanzu ma’aikatar tsaron Amurka ba ta bayar da wani karin haske kan mutuwar tasa ba. A ‘yan watannin da suka gabata kasar ta sanya ladan dala miliyan daya kan duk wanda ya bayar da bayanan da za su kai ga kama Hamza Bin Laden, mai shekara 30. A lokacin sun ce yana kokarin zamowa wani babban kusa a shugabancin kungiyar ta Al-ka’ida. Sun kara da cewa ya yi amfani da sakonnin murya da bidiyo domin yin kira a kaiwa Amurka da kawayenta hari – domin ramuwar gayya ga kisan mahaifinsa. A shekarar 2011 ne dakarun Amurka suka kashe Osama Bin Laden – wanda aka zarga da taimakawa wurin shirya hare-haren 11 ga watan Satumba bayan shafe shekara 10 ana nemansa. An kuma gano wasu takardu a gidan da aka kashe shi a Pakistan, wanda aka ce shi ya rubuta, inda ya ce yana horas da dan nasa domin ya gaje shi.