Jam’iyyar APC a karamar hukumar Bebeji ta jihar Kano ta kori dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Bebeji da Kiru, Abdulmumin Jibrin Kofa, tare da neman uwar jam’iyyar ta kore shi gaba daya.
A wata sanarwa da shugaban jam’iyyar na karamar hukumar Bebeji, Suleiman Gwarmai, ya sanya wa hannu, ya ce an dakatar da dan majalisar mai wakiltar ne a mazabarsa, saboda yana yi wa jam’iyyar zagon-kasa.
Alhaji Suleiman ya ce an dauki matakin ne bayan da wani kwamiti mai mutane bakwai da jam’iyyar ta kafa bayan da ta samu korafi a kan dan majalisar, ya yi bincike ya kuma mika rahotonsa.
Kawo Abdulmumini Jibrin bai mayar da martani ba
kan wannan sanarwa. BBC ta tuntube shi a waya amma bai amsa kiran ba.
A baya-bayan nan dan majalisar ya samu kansa cikin rikicin siyasa tsakaninsa da wasu gaggan jam’iyyar a Kano. Kuma rahotanni sun ambato shi yana cewa yana shirin barin majalisa domin komawa jami’a saboda yana so ya zama farfesa.
Yana kuma fuskantar shari’a a kotun sauraran kararrakin zabe ta jihar Kano inda mutumin da ya kayar a zaben 2019, Ali Datti Yako, ke kalubalantar nasarar tasa.
Shugaban APC a Bebeji ya ce: “Bayan karbar korafin da shugabannin kwamitin zartarwa na jam’iyyar APC na karamar hukumar Bebeji, suka yi, an kafa kwamitin mutane bakwai domin gudanar da binciken dukkanin korafe-korafen da mai zargin ya yi,” In ji shugaban.
Ya kara da cewa: “Bayan cikakken bincike, kwamitin ya mika rahotansa da kuma shawarwari ga shugabannin zartarwa na jam’iyya a karamar hukumar, wadanda daga nan suka yi taro tare da bayyana wadannan matakai, kamar haka:
Bayan tabbatar da dan majalisa Hon. Abdulmuminu Jibrin Kofa, ya aikata abubuwa da dama da suka saba wa kundin tsarin mulkin, kama daga doka ta 21, sakin layi na A (ii) (V), da kuma sashe na (Vii), shugabannin zartarwar sun amince da rahoton.
Saboda haka sun dakatar da Hon. Kofa ba tare da wani bata lokaci ba, har tsawon wata 12.”
Sanarwar ta kara da cewa bayan haka kuma, shugabannin sun kuma amince da shawarar kwamitin ta bukatar shugabannin jam’iyya na jihar ta Kano su ba wa uwar jam’iyya ta kasa shawarar ta kore shi daga cikinta saboda laifukan da ya aikata daban-daban.
Abdulmumini Jibrin ya sha samun kansa a rikicin siyasa a matakin jiha da kuma majalisa, inda har aka taba dakatar da shi a majalisa ta takwas da ta shude.
Comments
Post a Comment