Skip to main content

An ‘kashe’ dan Osama Bin Laden

Rahotanni daga kafafen yada labaran Amurka sun ce an kashe Hamza Bin Laden, dan tsohon shugaban kungiyar Al-ka’ida marigayi Osama Bin Laden.

Har yanzu ma’aikatar tsaron Amurka ba ta bayar da wani karin haske kan mutuwar tasa ba.

A ‘yan watannin da suka gabata kasar ta sanya ladan dala miliyan daya kan duk wanda ya bayar da bayanan da za su kai ga kama Hamza Bin Laden, mai shekara 30.

A lokacin sun ce yana kokarin zamowa wani babban kusa a shugabancin kungiyar ta Al-ka’ida.

Sun kara da cewa ya yi amfani da sakonnin murya da bidiyo domin yin kira a kaiwa Amurka da kawayenta hari – domin ramuwar gayya ga kisan mahaifinsa.

A shekarar 2011 ne dakarun Amurka suka kashe Osama Bin Laden – wanda aka zarga da taimakawa wurin shirya hare-haren 11 ga watan Satumba bayan shafe shekara 10 ana nemansa.

An kuma gano wasu takardu a gidan da aka kashe shi a Pakistan, wanda aka ce shi ya rubuta, inda ya ce yana horas da dan nasa domin ya gaje shi.

Comments

Popular posts from this blog

Kaifin basira da magunguna 4 da kwallon kankana ke yi a jikin dan Adam

Kankana ta kasance daya daga cikin 'ya'yan itatuwa mafi shahara a doron kasa kuma mutane da dama su kan yi santi kwarai yayin kwankwadar ruwanta musamman wadanda kwayoyin halittun su masu bambance dandano ke aiki kwarai. A yayin da kankana ta kasance cikin dangin itatuwa da ake kiransu 'ya'yan duma, 'ƙwallayen cikin da sun ƙunshi sunadarai masu tarin alfanu da kuma tasiri wajen inganta lafiyar jikin dan Adam. Sai dai kash da yawan mutane su kan watsar da ƙwallon kankana a sakamakon rashin sanin muhimmancin su wajen inganta lafiyar su. Wadannan ƙwallaye da kankana ta kunsa suna da arzikin sunadarai da suka hadar da fatty acids, proteins, minerals (magnesium, poatssium, manganese, iron, zinc, phosphorus, copper), vitamin B (thiamine, niacin, folate) da kuma calories.  Bincike ya tabbatar da cewa, ana amfani da ƙwallayen kankana a matsayin abinci a yankunan nahiyyar Asia da kuma wasu yankunan daular Larabawa ta Tsakiya inda ake gasa su kuma kwadanta da ganyayya...

MUSIC : Ali Jita - Mairo Almakura (Giwa)

Wannan wata sabuwa waka ce da ali Jita ya rerawa matar Tanko almakura wanda tayi kyau sosai. Wanda shine munka kawo muku domin saurarenku. DOWNLOAD MP3 Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com