Kafin rasuwar Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam (Allah Ya Jikansa Ya Gafarta Masa) ya sha jan hankalin hukumomin tsaro akan fitinar jihar Borno, aka yi biris ba tare da daukar mataki ba. Har yanzu Najeriya na dandana kudarta akan wannan fitina. Jaridar Daily Trust ta taba yin wani rahoto akan yadda ake hada baki da 'yansanda ana dillancin bindigo a jihar Zamfara, rashin daukar mataki akan lokaci yau ga jihar ta zama Kabari-Salamu-Alaikum. Rahotanni na ta yawo a kafar sada zumunta da jaridu na wasu bakin-haure da suka yada zango a jihar Sakkwato dauke da manyan makamai. Suna yi kira ga mutane da su bi tsarin da suka zo musu da shi. Yin biris da wannan rahoton ba tare da binciken sahihancin sa ba, babban sakaci ne gami da sakarcin mahukuntan kasa. A bincika a kuma dauki matakin gaggawa tun kafin wankin hula ya kai mu yin dare. Na tabbatar da yau rahoton sirri aka samu za a kai hari Abuja, da tuni an dauki matakin gaggawa. Kamar yadda da rahoton kai wa Tambuwal hari ko Wammak...