Skip to main content

Kafin A ZUubar Da Jinin Talakawan Jihar Sakkwato....(karanta)



Kafin rasuwar Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam (Allah Ya Jikansa Ya Gafarta Masa) ya sha jan hankalin hukumomin tsaro akan fitinar jihar Borno, aka yi biris ba tare da daukar mataki ba. Har yanzu Najeriya na dandana kudarta akan wannan fitina.

Jaridar Daily Trust ta taba yin wani rahoto akan yadda ake hada baki da 'yansanda ana dillancin bindigo a jihar Zamfara, rashin daukar mataki akan lokaci yau ga jihar ta zama Kabari-Salamu-Alaikum.

Rahotanni na ta yawo a kafar sada zumunta da jaridu na wasu bakin-haure da suka yada zango a jihar Sakkwato dauke da manyan makamai. Suna yi kira ga mutane da su bi tsarin da suka zo musu da shi.

Yin biris da wannan rahoton ba tare da binciken sahihancin sa ba, babban sakaci ne gami da sakarcin mahukuntan kasa. A bincika a kuma dauki matakin gaggawa tun kafin wankin hula ya kai mu yin dare.

Na tabbatar da yau rahoton sirri aka samu za a kai hari Abuja, da tuni an dauki matakin gaggawa. Kamar yadda da rahoton kai wa Tambuwal hari ko Wammako aka samu da tuni an dauki mataki. Don haka a gaggauta daukar matakin kare rayukan talakawan jihar Sakkwato ko domin sake zaben ku a Gwamna da Sanata.

Wani abin ban haushi da matasan Sakkwatawan shine yadda suka rika bi duk titin da Tambuwal ya bi suna sharewa saboda ya bar APC ya koma PDP amma a halin yanzu sun kasa yin ayari zuwa gidan Sarkin Musulmi ko Majalisar jiha ko gidan Gwamnati domin kira a bincika wannan batu.

Kamar yadda suka kasa amfani da kafafen sadarwa na zamani domin kaddamar da kiraye-kiraye ga 'yan Majalisar wakilai na tarayya da Sanatocin su akan su kai kukan su ga hukumomin tsaron kasa a bincika wannan batu gami da daukar mataki.

Yau abin Allah Ya kiyaye idan fitinar ta zo 'ya'yan Talakawa ne za su fi kowa shan azaba. Ku duba abinda ya ke faruwa a jihar Zamfara. Ku tashi ku ja hankalin 'yan siyasar Ku yanzu ba wannan ne matsalar su ba, ba a jihar Sakkwato suke da zama ba. Matsalar su a halin yanzu KURI'UN Ku a zabe mai gabatowa.

Shin a jihar Zamfara kun ga ko kun ji ana Garkuwa ko kashe 'ya'yan Manya. Ganin Buzu a Masallaci ya isa darasi ga Tunkiya.

Daga: Maje El-hajeej Hotoro

Comments

Popular posts from this blog

Kaifin basira da magunguna 4 da kwallon kankana ke yi a jikin dan Adam

Kankana ta kasance daya daga cikin 'ya'yan itatuwa mafi shahara a doron kasa kuma mutane da dama su kan yi santi kwarai yayin kwankwadar ruwanta musamman wadanda kwayoyin halittun su masu bambance dandano ke aiki kwarai. A yayin da kankana ta kasance cikin dangin itatuwa da ake kiransu 'ya'yan duma, 'ƙwallayen cikin da sun ƙunshi sunadarai masu tarin alfanu da kuma tasiri wajen inganta lafiyar jikin dan Adam. Sai dai kash da yawan mutane su kan watsar da ƙwallon kankana a sakamakon rashin sanin muhimmancin su wajen inganta lafiyar su. Wadannan ƙwallaye da kankana ta kunsa suna da arzikin sunadarai da suka hadar da fatty acids, proteins, minerals (magnesium, poatssium, manganese, iron, zinc, phosphorus, copper), vitamin B (thiamine, niacin, folate) da kuma calories.  Bincike ya tabbatar da cewa, ana amfani da ƙwallayen kankana a matsayin abinci a yankunan nahiyyar Asia da kuma wasu yankunan daular Larabawa ta Tsakiya inda ake gasa su kuma kwadanta da ganyayya...

64 Best Free WordPress Blog Themes for 2020

Are you looking for a free WordPress blog theme for your website? There are thousands of free blog themes for WordPress, making it hard for beginners to choose between all the different options. The best WordPress themes can be tough to find. Your free theme needs to be reliable and easily customizable. In this article, we have hand-picked some of the best free WordPress blog themes that you can use on your site. Getting Started with WordPress First, you need to make sure that you are using the best blogging platform . Self-hosted WordPress.org is the perfect platform to start your blog because it gives you lots of freedom, flexibility, and control. We have a useful guide on the difference between WordPress.org and WordPress.com . WordPress.org is open source. It comes with support for thousands of free templates (called themes) and extensions (called plugins) that help you grow your blog faster. Take a look at our article on why you should use WordPress to learn more. You can...

30+ Best WordPress Business Themes (2020)

Are you looking for the best WordPress business themes? While there are many free and premium WordPress themes available on the internet, not all of them are suitable for your business website. In this article, we will share some of the best WordPress business themes that you can use. Creating a Business Website with WordPress WordPress is the most popular website builder in the market. This is why many big brands use WordPress for their sites. You will find 2 types of WordPress websites on the internet. WordPress.com, which is a hosted solution, and WordPress.org, which is a self-hosted platform. Check out our complete article on WordPress.com vs WordPress.org for more details. For a business website, you need to use self-hosted WordPress.org because it is highly flexible and comes with full WordPress features. But first, you will need a domain name and a WordPress hosting account. A domain name is your website URL (like wpbeginner.com), and WordPress hosting is the storage...