Tunda Ka Kasa Magana Akan Wanda Aka Yankewa Hukuncin Kisa A Kano Ba Zamu Zaɓe Ka Ba, Ƴan Kudu Suka Faɗawa Atiku
Wasu ƴan Kudancin Najeriya da dama na caccakar tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP a zaɓen shekarar 2019 da ya gabata, Atiku Abubakar saboda ƙin yin magana akan hukuncin kisan da aka yankewa matashin da yayi batanci ga Annabi (S.A.W) a Kano.
Sun ta yin magana a shafukansu na Twitter inda suke neman Atikun yayi magana akan lamarin. Mun fahimci kiran ya ƙara ƙamari bayan da Atiku ya taya ƙungiyar Arsenal murnar nasarar da ta samu akan Liverpool jiya, inda wasu ke cewa ba akan wannan suke so yayi magana ba.
Dokin karfe na wallafa,wani me suna Nwoke NKwerre ya bayyana cewa Atiku muna so mu ji ta bakinka kan hukuncin kisa da aka yankewa matashinnan a Arewa. Wasu na ganin shirun ka kamar yana nuna ka amince da hukuncinne.
Hakanan wani me suna Malachy Odo II ya bayyana cewa Atiku na magana akan komai amma banda maganar hukuncin kisa da aka yankewa matashi a Kano saboda kalaman ɓatanci.
Ya kara da cewa, shirun shi ya nuna cewa shima yana da tsatstsauran ra’ayi kamarsu ko kuma baya son ya ɓata musu rai dan nan gaba zai nemi ƙuri’arsu.
Itama wata ta mayarwa da Atiku martani bayan da ya taya Arsenal murna da cewa, har yanzu muna jiran abinda zaka ce kan maganar hukuncin kisa da akawa matashi a Kano.
Comments
Post a Comment