Daga bbchausa.com
Yanzu lokaci ne da ake fuskantar tsananin zafin rana a wasu yankuna na Kudu da Hamadar Sahara da suka hada da garuruwan da ke arewacin Najeriya da Jamhuriyyar Nijar.
Wannan ya sa muka tuntubi masana harkar lafiyar abinci don su bayar da shawarawari kan irin abubuwan da ya kamata a dinga ci da sha yayin da ake fuskantar tsannain zafin rana.
Zafi yana sa gajiyadda kishirwa, yna kuma kona ruwan jiki. Don haka jiki na bukatar abincin sha mai sanyi wanda zai sa a mauatr da ruwan da ke konewa a kuma sami yanayi mai sanyi
Jiki kan rasa kusan lita biyu zuwa biyu da rabi na ruwa a duk rana ta hanyar yi gumi da shan numfashi da fitsari da bahaya.
Don haka a kalla ana bukatar a sha kofi shida zuwa takwas na ruwa a rana ko sauran abubuwa masu dauke da ruwa a cikinsu.
Malama Maijidda Badamasi Shu'aibu Burji wata kwarariya ce kan fannin abinci kuma malama a makarantar sakandaren 'yan mata da ke Darmanawa a Kano, kuma ta bayyana jerin abubuwan da ya kamata a dinga ci a wannan yanayi.
1. Gurji - Gurji kayan lambu ne da ke kunshe da saindarai daban-daban masu amfani da kare lafiyar jiki da fata
2. Mangwaro - Yana kare konbewar ruwan jiki.
3. Manyan lemon tsami - Yana kunshe da sinadaran bitamin C da B da sindaran Mineral kamar Calcium da Phosporous da Magnesium.
Ana iya sarrafa lemon tsami ta hanyar matse shi da kara masa ruwa da sanya sikari daidai idan ana bukata.
4. Kankana - Kashi 95 cikin 100 na kankana ruwa ne kuma shanta na kawar da kishi ruwa sosai.
5. Tsamiya - Ita ma tana daga cikin 'ya'yan itacen da suke taimakawa wajen inganta jiki lokacin zafi. Ana iya dafa ta tare da masoro da na'ana a tace ruwan a sanya dan sikari idan ana bukata a dinga sha.
6. Ruwan Rake - Ya kunshi sinadarai kamar Potatssium da Glucose da Calsium da Magnesium, sannan yana da amfani wajen kara wa jiki ruwa.
7. Ruwan Kwakwa - Shi ma ruwan da ke cikin kwakwa yana da muhimmanci a dinga sha lokacin yanayin zafi.
8. Gwaiba - Malam Maijidda ta ce gwaiba ma wani muhimmin kayan marmari ne da jiki ke bukata miusamman a lokacin zafi, saboda sinadaran da take dauke da su kan masu inganta yanayin jiki ne.
10. Abarba - Ita ma tana da sinadari masu saurin sa abinci ya narke da kuma ruwa sosai a cikinta.
11. Tumatur - Kashi 94 na tumatur ruwa ne. Za a iya cin sa haka ko a markada ko a saka shi cikin abinci.
12. Korayen ganyayayaki - Kusan kashi 80 zuwa casa'in nasu ruwa ne, wanda yake sawa su narke nan da nan idan an ci su. Hakan na sawa su sanyaya jiki. Ganyayyaki sun hada da kamar su zogale da latas da lamsur da alayyahu da sauran su.
Comments
Post a Comment