Skip to main content

Abinda Yasa Nayi Wakar 'Jarumar Mata' ~ Hamisu Breaker

Tun bayan da bidiyon gasar rawar matan aure ya zama ruwan dare gama duniya a arewacin Najeriya da aka yi lokacin bikin sallah, sai hankalin mutane ya koma kan wakar da ta sa suka taka rawar.
Wannan waka dai takenta shi ne 'Jarumar Mata' wadda Hamisu Breaker Dorayi ya rera.
Duk da cewa mawakin ya ce ya yi wakar ne a karshen shekarar 2019, kuma ya sake ta a farkon 2020, za a iya cewa dubban mutane ba su san ta ba sai a makon bikin karamar sallah, bayan da wasu matan aure suka yi yayin yin rawarta.
A wata hirar bidiyo kai tsaye da BBC Hausa ta yi da Hamisu Breaker a shafinta na Instagram, matashin mawakin ya ce wannan gasa da mata suka yi ba karamin farin jini ta kara masa shi da wakar ba.
Ya ce: ''Wakar ta yi matukar tashe a lokacin da ta fito amma na yi tunanin ma tashenta ya dan ja baya, kawai kwanan nan sai na ji ta sake karade duniya.''

'Abin da ya sa na yi wakar'

Hamisu BreakerHakkin mallakar hotoINSTAGRAM/HAMISU_BREAKER_DORAYI
Image captionBreaker ya ce yana gab yin aure
"Abin da ya sa na yi wakar jarumar mata na yi duba ne kan mutane. Idan zan yi waka ina duba halayyar mutane ne, misali wani na zurfafawa wajen soyayya wasu kuma ba su da.
''Kuma na ga na kwana biyu ban yi wa masoya waka ba, shi ya sa na ce bari nai musu. Ba budurwata na yi wa ba gaskiya."
'' Idan zan yi waka ba na tunanin samari da 'yan mata kawai, ina farawa ne tun daga kan tsoho mai shekaru da yawa, haka-haka har zuwa kan masu karancin shekaru yadda kowa zai ji wani abu da ya dangance shi."
Hamisu ya ce ya tsaya tsaf ne ya zabi kalaman da ya yi amfani da su a cikin wakar. ''Alal misali baitin farko da nake cewa ashe da rai nake sonki Jaruma ba da zuciyata ba. Kin ga hakan na nufin wannan soyayyar sai ranar da aka mutu za a daina ta tun da ba da zuciya mai sauye-sauye ake yin ta ba.

Na ji matukar dadi

To ko yaya Breaker ya ji bayan da wakar ta sake shahara a baya-bayan nan?
''Ban taba tsammanin wakar za ta zaburar da matan aure ba har su yi gasa a kanta. Na yi ne don masoyana da kuma fatan za ta shahara, sai kuma ga shi ta yi irin farin jinin da ban yi tsammani ba,'' in ji shi.
Ya ci gaba da cewa: ''A lokacin da na ga mata sun fara gasar sai na ji dadi sosai, na ce na zama daya daga cikin mutanen da suke ba da gudunmuwa a cikin gyaran aure. Ban taba tunanin ganin haka ba gaskiya."
A ranar ina ta tunanin kamar na sanya bidiyon matan a shafina, amma kuma sai na yi tunanin hakan bai dace ba. Amma na ji dadi kuma na musu fatan alkhairi.
Breaker ya ce bai san adadin mutanen da suka kira shi a waya don sanar da shi cewa ya ga yadda wakarsa ta yi tashe a wannan dan tsakanin na bikin sallah ba.
BBC ta tambaye shi kan ra'ayinsa kan rawar matan aure a bidiyo a saka a shafukan sada zumunta.
Sai ya ce duk da dai a tunaninsa sanya rawar a social media din na iya zama kuskure. Amma tun da ni ba malamin addini ba ne ba zan iya fashin baki kan hakan ba.

Wakar Jarumar Mata

Wakar dai tana da baituka tara ne masu sadara hudu, kuma tana karewa da kafiya.
Hamisun ya ce baitin da ya fi so shi ne na bakwai da yake cewa:
''Yau ga ni a ruwa kusa da kasa zo ki ceci karkona
Komai da mafita kada ki saba da furta bankwana
Ina ji ina gani yadda nake sonki ya fi karfina
Na san a duniya da wanda yake janye duk tunanina.

Wane ne Hamisu Breaker?

Hamisu BreakerHakkin mallakar hotoCHIZO PHOTOGRAPHY
Image captionAn haifi shahararren mawakin Hausan ne a shekarar 1993 a Kano
Sunansa Hamisu Breaker Dorayi, kuma dan asalin jihar Kano ne, shekarunsa 27.
Ya yi karatun firamare da sakandare a unguwar Dorayi. Ya fara waka tun yana makarantar Islamiyya lokacin yana yaro, amma a shekarar 2016 aka fara sanin sa.
Zuwa yanzu ya yi wakokin da shi kansa ya ce bai kirga yawansu ba.Ya yi wakoki irinsu "So", da "Shimfidar Fuska" da "Hauwa" da sauransu.

Comments

Popular posts from this blog

25 Awesome iPhone App Icon Packs to Customize Your Home Screen

With the release of iOS 14, Apple made it possible to customize the app icons on your iPhone's Home Screen without worrying about duplicates. Of course, most of us aren't graphic designers, so we need to rely on iOS app icon packs made by other people to change the look of our Home Screen. We've scoured the web to find the coolest, most unique, and best-designed iOS app icon packs for you to download. Before You Customize Your iOS App Icons There are a few important points you need to know before you customize the app icons on your iPhone Home Screen: It's time-consuming: For every app icon you want to change, you need to create a new shortcut in the Shortcuts app, then add it to your Home Screen and hide the original app. If you have a lot of apps, this could take hours. Custom icons don't show notification badges: Customized app icons act as a shortcut to the original app. For this reason, they don't show red notification badges like normal apps. The o...

The 9 Different Types of NFTs

Jack Dorsey, the creator of Twitter, sold the world's first tweet for $2.9 million; this bit of news is what introduced most people to the world of NFTs (Non-Fungible Tokens). Now all the rage, NFTs are being bought and sold like priceless pieces of art. The NFT market is seemingly swarming with digital Mona Lisas, but the question is: besides tweets and pictures, what other types of NFTs are there in the wild? Let's take a dive into the world of NFTs and find that answer. First Off: What Are NFTs? Digital media can be replicated easily and redistributed; however, try making an honest-to-goodness copy of the Mona Lisa down to the brush strokes and the original paper. Think of NFTs as digital non-replicable pieces of art. These are properties that can not be copied or replaced at all. Sure, the media itself can be copied and posted to a person's social media, but the buyer will retain ownership of the NFT, regardless. Hitting Ctrl + C on an NFT and posting it is the equi...

The 7 Best Wired Headphones

Premium pick Sony WH1000XM4/B Over-Ear Headphones See On Amazon Brand Sony Battery Life 30 hours Material Synthetic leather Editors choice PeohZarr On-Ear Headphones See On Amazon Brand PeohZarr Material Synthetic leather Bluetooth No Best value Vogek On-Ear Headphones See On Amazon Brand Vogek Material Protein leather Bluetooth No Grado SR80e Prestige See On Amazon Brand Grado Battery Life N/A Material Leather Sony MDR-XB50AP Extra Bass See On Amazon Brand Sony Bluetooth No Additional Tips Yes Summary List 9.20 /10 1. Premium pick: Sony WH1000XM4/B Over-Ear Headphones 9.00 /10 2. Editors choice: PeohZarr On-Ear Headphones 9.00 /10 3. Best value: Vogek On-Ear Headphones 9.00 /10 4. Grado SR80e Prestige 9.00 /10 5. Sony MDR-XB50AP Extra Bass 8.60 /10 6. Panasonic ErgoFit 9.20 /10 7. Apple Ear...