Daga Dr Idris Ahmed PhD Cryptology
Kwararren Likitan gargajiya Dr. Jawa Ibrahim Muhammad daga jihar Yobe ya gano rigakafi da maganin gargajiya da zai iya kashe kwayoyin cutar Coronavirus
Yanzu haka, hukumar dake magance cututtuka masu yaduwa ta Nigeria NCDC, da kwamitin fadar shugaban kasa akan yaki da cutar Coronavirus da gwamnan jihar Yobe sun karbi maganin da Dr Jawa Ibrahim ya gano, suna jiran sakamakon bincike da amincewar masana kiwon lafiya kafin a fara amfani da maganin a hukumance
Dr Jawa yayi digiri na biyu (Masters) daga kwalejin horar da aikin Likita WFAS Institute Beijing, sannan yayi digiri na uku (PhD) a Holistic Medicine (African traditional Medical Science) a University of Kolkata.
Dr. Jawa ya shafe shekaru 40 a wannan fanni na Likitanci, yana samar da magungunan da suke magance miyagun cutuka, shine ya samar da wasu magunguna guda hudu da suke karawa huhu karfi tare da magance abinda cutar Coronavirus ke haifarwa na toshe kofofin shigar iska zuwa cikin huhu wanda yake haddasa daukewar numfashi da mutuwa
Dr. Jawa shine zababben sakataren kungiyar masu maganin gargajiya na jihar Yobe, kuma shine shugaban kungiyar masu maganin gargajiya na Nigeria gabaki daya, yana da wata makaranta mai karfi da take bada shaidar karatun Diploma akan maganin gargajiya na mutanen Afirka da China, wanda ya samu lasisi da amincewa daga hukumar kula da kiwon lafiya na gwamnatin Nigeria
Muna fatan Allah Ya sa a dace, Allah Ya kawo mana karshen wannan masifa Amin
Comments
Post a Comment