Daga Dr Idris Ahmed PhD Cryptology Kwararren Likitan gargajiya Dr. Jawa Ibrahim Muhammad daga jihar Yobe ya gano rigakafi da maganin gargajiya da zai iya kashe kwayoyin cutar Coronavirus Yanzu haka, hukumar dake magance cututtuka masu yaduwa ta Nigeria NCDC, da kwamitin fadar shugaban kasa akan yaki da cutar Coronavirus da gwamnan jihar Yobe sun karbi maganin da Dr Jawa Ibrahim ya gano, suna jiran sakamakon bincike da amincewar masana kiwon lafiya kafin a fara amfani da maganin a hukumance Dr Jawa yayi digiri na biyu (Masters) daga kwalejin horar da aikin Likita WFAS Institute Beijing, sannan yayi digiri na uku (PhD) a Holistic Medicine (African traditional Medical Science) a University of Kolkata. Dr. Jawa ya shafe shekaru 40 a wannan fanni na Likitanci, yana samar da magungunan da suke magance miyagun cutuka, shine ya samar da wasu magunguna guda hudu da suke karawa huhu karfi tare da magance abinda cutar Coronavirus ke haifarwa na toshe kofofin shigar iska zuwa cikin hu...