Skip to main content

Na Koyi Darasi A fim Dina Na Farko - Jaruma Asabe Madaki

Daya daga cikin jaruman Kannywood mata wanda ke tashe a yanzu a masana'antar fina-finan Hausa da na turanci Asabe Madaki ta bayyana ilimi da karuwar da ta samu a fim din ta na farko a Kannywood mai suna "SARAUNIYA".

Jarumar ta bayyana hakan ne lokacin da suke tattaunawa da majiyar mu dangane da Kannywood da kuma abun da ya jawo hankalin ta na fara fitowa a fina-finan Hausa.

Inda ta fara mana da cewa” da farko dai ina godiya ga gwamnatin jihar kaduna da jihar Kano a kan irin gudummawar da suke bayar wa ga masana'antar fina-finan Kudu da na Arewa. Kuma kafin na fara yin waka da shirin fim ni babbar lauya ce, na yi karatun lauya kuma yar kasuwa ce ni, kuma ina da kamfanin daukar shirye-shirye nawa na kai na wanda yanzu haka ina kokarin na ga na fara bada umarni da kuma daukar nauyin shirye-shirye a nan ba da jimawa ba. A fannin fim dina kuwa a gaskiya na samu ilimi da karuwa sosai a fim din da na fara fitowa a Kannywood mai suna SARAUNIYA duk da cewa ba shi ne fim di na ne farko ba a duniya, amma ya zama daya daga cikin fina-finan da nake alfahari dasu, kasancewar shi fim mai ma'ana wanda ya ke dauke da darussa tare da fadakarwa da yawan gaske a cikin sa. Abun da shirin ke kunshe da shi kuwa shi ne, na farko an kara tunatar da ni a kan ‘ya’ya mata suma za su iya daukar duk wani abun da namiji zai dauka a rayuwa, kamar mulki, gadon gida ko kuma kula da wata dukiya na iyayen ta indai  har an bata tarbiyya mai kyau kuma an nuna mata abubuwa da yawa. Toh zata iya kulawa da komai kamar yadda namiji zai yi tun da ita mutun ce kamar kowa." A cewar Asabe Madaki.

Ta kara da cewar”Shirin Sarauniya ya kara wayar da mutane kai a kan su dai na mayar da yara mata gefe a fannin mulki ko wani mukami saboda yin ba dai dai, duk wani abun da da namiji zai yi mace ma za ta iya yi watakil fiye dashi. Kuma shirin ya nuna cewa zaman lafiya abu ne mai kyau, duk wani abun da kaga Allah ya baiwa wani toh ba wanda ya isa ya kwace maka saboda Allah ne ya baka duk wuya duk rintsi naka ne. Kuma mutun ya zama adalin shugaba a kan duk wani mukamin da Allah ya bashi. Kuma ina farin ciki a kan irin cigaban da Kannywood ta samu a yanzu saboda kullum suna kokarin gyara fina-finan su, saboda yanzu muna shiga manya gasar fim ta duniya da fina-finan mu, toh dalilin hakan yasa kowa ya ke kan jiki kan karfi wajen gyara aikin sa. Kuma Kannywood za ta kai inda ba a taba tsammani ba wasu daga cikin cigaban suna, nan gaba za a samu jarumai masu ilimi, manyan sinimomi, manhajoji na kallon fim a duniya da kuma abubuwa da daman gaske”. Inji Jarumar.

Daga karshe ta yi wa masoyan ta godiya tare  da fatan alheri da kuma albishir a kan cewa nan gaba za ta yi kokari ta kawo masu  duk abun da suke so tare da sababbin wakoki masu fadakarwa da nishadantar wa da za ta yi a nan gaba.

Comments

Popular posts from this blog

64 Best Free WordPress Blog Themes for 2020

Are you looking for a free WordPress blog theme for your website? There are thousands of free blog themes for WordPress, making it hard for beginners to choose between all the different options. The best WordPress themes can be tough to find. Your free theme needs to be reliable and easily customizable. In this article, we have hand-picked some of the best free WordPress blog themes that you can use on your site. Getting Started with WordPress First, you need to make sure that you are using the best blogging platform . Self-hosted WordPress.org is the perfect platform to start your blog because it gives you lots of freedom, flexibility, and control. We have a useful guide on the difference between WordPress.org and WordPress.com . WordPress.org is open source. It comes with support for thousands of free templates (called themes) and extensions (called plugins) that help you grow your blog faster. Take a look at our article on why you should use WordPress to learn more. You can...

The Best 10 Social Media Platforms for Photographers to Flaunt Their Talent

Social media offers an excellent opportunity for photographers to connect with potential clients. In the digital era, it's a great asset. By showcasing your work on these networks, you can reach new audiences. Whether you are a professional or freelance photographer, the following social platforms will help you show off your work and get the right people to take notice... 1. Behance Behance is a classic portfolio publishing network that functions like a LinkedIn for creatives. Designed by Adobe, this is one of the best photography networking sites currently out there. The platform is ideal for sharing your portfolio and favorite images, allowing other Behance users to like and comment on your photos. By learning from their feedback and professional critiques, you can improve your work. The coolest feature of Behance is that it lets you find professional gig opportunities right on the platform. With your portfolio already available on the site, getting work becomes effortless. ...

25 Awesome iPhone App Icon Packs to Customize Your Home Screen

With the release of iOS 14, Apple made it possible to customize the app icons on your iPhone's Home Screen without worrying about duplicates. Of course, most of us aren't graphic designers, so we need to rely on iOS app icon packs made by other people to change the look of our Home Screen. We've scoured the web to find the coolest, most unique, and best-designed iOS app icon packs for you to download. Before You Customize Your iOS App Icons There are a few important points you need to know before you customize the app icons on your iPhone Home Screen: It's time-consuming: For every app icon you want to change, you need to create a new shortcut in the Shortcuts app, then add it to your Home Screen and hide the original app. If you have a lot of apps, this could take hours. Custom icons don't show notification badges: Customized app icons act as a shortcut to the original app. For this reason, they don't show red notification badges like normal apps. The o...