Tsohuwar jarumar Kannywood, Mansura Isa ta wadda ta kasance guda daga cikin jarumai mata wadanda suka taka muhimmiyar rawa a Kannywood tun duniya ta na kwance. Jaruma ce da ta yi tashe a wancan lokacin domin idan a na kiran sunayen jarumai mata za a sakata a jerin farko na manyan jarumai mata na lokacin. Sai dai kuma tun bayan auren ta da Jarumi Sani Danja a ka dai na jin duriyar ta sai daga baya bayan nan. Mansura Isa ta koma gefe guda inda ta bude cibiyar tallafawa marayu mai suna Todays Life Foundation, wadda ta yi kaurin suna wajen tallafawa marayu marasa lafiya da dai sauransu. Har ila yau jarumar ta na daya daga cikin matan dake tofa albarkacin bakin su a duk lokacin da wata matsala ta taso domin samun gyara a cikin al’umma baki daya. Misali akwai lokacin da a ka samu sabani tsakanin Sadiya Haruna da saurayin ta Isa A Isa, wadda ta shiga cikin maganar tare da yin sulhu, duk da hakan ba ta yiwu yadda yakamata ba, amma ta zaunar da Sadiya ta nu na mata illar yin hakan. ...