Skip to main content

Waka Ko Fim Adam A Zango Ya Koma Yi Legas

Fitatcen Jarumin Arewacin Najeriya Adam A Zango ya Kara daka tsallen ficewa daga masana’antar fim din Arewacin Nigeria ya koma garin Legas da harkokin sa na wake-wake, bayan ficewarsa daga masana’antar fim ta Kannywood inda ya koma cin gashin kansa.

Jaridar Aminiya ce ta bayyana cewa Jaruman ya yi hijira zuwa garin legas da zama tare da kuma maida duk harkokin sa can kudancin Najeriya saboda rashin mamora da ta rage a masana’antar fim ta Hausa sai zalinci da sharri da kuma ci masa mutunci da a ke yi.

A watannin da su ka gabata ne dai Adam A Zango ya bayyana ficewarsa daga masana’antar Kannywood sakamakon hatsaniya da a ke zargin ta shiga tsakanin sa da hukuma tace fina-finai da Dab’i ta Jihar Kano. Tun a wancan lokacin Jarumin ya mayar da hankalinsa wajen yin wakokinsa da finafinai a matsayin sa na ba dan Kannywood ba.

Bayan ficewarsa daga Kannywood, Adam Zango ya fito da wata kafar yanar gizo a kan dandalin youtube domin tallata finafinan sa a duniya, inda ya ke karbar Naira Dubu guda a wajen masu sha’awar fim din sa wanda daga bisani ya ke turawa wadanda su ka biya kudi sakon samun shiga dandalin fim din na sa. Wannan kafar kasuwanci ta Adamu dai ya nade ta ne da Allah ya isa, inda ya yiwa wasu da ya ce sun yi masa kutsen kallon fim din sa ba tare da sun biya kudi ba.

A wannan sabuwar hijirar ta Adam Zango zuwa garin Ikko ya bayyanata ne a faifan bidiyo inda ya ke jaddadawa masoyan sa cewa “Ni yanzu ma na tattara na koma jihar legas da zama don na ci gaba da sabgogina, idan kun ganni a arewacin Najeriya waka nazo yi ko biki ko kuma wani abu da a ka gayyace ni idan kuma na gama na dawo. Amma ba fim ba kuma duk wanda ya ke masana’antar Kannywood ya san cewa ni yanzu ba Dan fim ba ne.” Inji Adam A Zango

To ko dai Adamu ya bi sahun abokan sana’arsa ne da ke gogayya a masana’antar finafinai ta Nollywood irin su Yakubu Muhammed da Sani Danger da su ke finafinai da wakokin turanci?

#NorthFlix

The post Waka Ko Fim Adam A Zango Ya Koma Yi Legas appeared first on ArewaBlog. NG™.

Comments

Popular posts from this blog

Kaifin basira da magunguna 4 da kwallon kankana ke yi a jikin dan Adam

Kankana ta kasance daya daga cikin 'ya'yan itatuwa mafi shahara a doron kasa kuma mutane da dama su kan yi santi kwarai yayin kwankwadar ruwanta musamman wadanda kwayoyin halittun su masu bambance dandano ke aiki kwarai. A yayin da kankana ta kasance cikin dangin itatuwa da ake kiransu 'ya'yan duma, 'ƙwallayen cikin da sun ƙunshi sunadarai masu tarin alfanu da kuma tasiri wajen inganta lafiyar jikin dan Adam. Sai dai kash da yawan mutane su kan watsar da ƙwallon kankana a sakamakon rashin sanin muhimmancin su wajen inganta lafiyar su. Wadannan ƙwallaye da kankana ta kunsa suna da arzikin sunadarai da suka hadar da fatty acids, proteins, minerals (magnesium, poatssium, manganese, iron, zinc, phosphorus, copper), vitamin B (thiamine, niacin, folate) da kuma calories.  Bincike ya tabbatar da cewa, ana amfani da ƙwallayen kankana a matsayin abinci a yankunan nahiyyar Asia da kuma wasu yankunan daular Larabawa ta Tsakiya inda ake gasa su kuma kwadanta da ganyayya...

64 Best Free WordPress Blog Themes for 2020

Are you looking for a free WordPress blog theme for your website? There are thousands of free blog themes for WordPress, making it hard for beginners to choose between all the different options. The best WordPress themes can be tough to find. Your free theme needs to be reliable and easily customizable. In this article, we have hand-picked some of the best free WordPress blog themes that you can use on your site. Getting Started with WordPress First, you need to make sure that you are using the best blogging platform . Self-hosted WordPress.org is the perfect platform to start your blog because it gives you lots of freedom, flexibility, and control. We have a useful guide on the difference between WordPress.org and WordPress.com . WordPress.org is open source. It comes with support for thousands of free templates (called themes) and extensions (called plugins) that help you grow your blog faster. Take a look at our article on why you should use WordPress to learn more. You can...

MUSIC : Ali Jita - Mairo Almakura (Giwa)

Wannan wata sabuwa waka ce da ali Jita ya rerawa matar Tanko almakura wanda tayi kyau sosai. Wanda shine munka kawo muku domin saurarenku. DOWNLOAD MP3 Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com