Skip to main content

A Matse Nake Da Nayi Aure - Jaruma Saima Muhammad

Ga duk wanda ya san harkar fina-finai ta Kannywood da dadewa, to ya san Saima Mohammed, fitacciyar 'yar wasan fim, amma a shekarun baya-bayan nan jarumar ta bace bat.
A wannan hira ta musamman da BBC Hausa, Saima, wacce 'yar asalin kasar Nijar ce, ta yi magana kan yunkurin da take yi na dawowa Kannywood, da dalilin da ya sa ta daina fitowa a dim da kuma dalilin da ya sa aurenta ya mutu.
Cikin dalilan da Saima ta fada na barin ta Kannywood har da cewa ta lura harkar fina-finan ba ta samun irin ci gaban da ya kamata duk da dadewar da aka yi, don haka ne ta janye jiki har sai abubuwa sun gyaru.

Jarumar ta kuma ce yanzu babban burinta a duniya shi ne ta yi aure, "a matse nake sosai da son yin aure. Ina fatan Allah ya kawo min miji.

Comments

Popular posts from this blog

Kaifin basira da magunguna 4 da kwallon kankana ke yi a jikin dan Adam

Kankana ta kasance daya daga cikin 'ya'yan itatuwa mafi shahara a doron kasa kuma mutane da dama su kan yi santi kwarai yayin kwankwadar ruwanta musamman wadanda kwayoyin halittun su masu bambance dandano ke aiki kwarai. A yayin da kankana ta kasance cikin dangin itatuwa da ake kiransu 'ya'yan duma, 'ƙwallayen cikin da sun ƙunshi sunadarai masu tarin alfanu da kuma tasiri wajen inganta lafiyar jikin dan Adam. Sai dai kash da yawan mutane su kan watsar da ƙwallon kankana a sakamakon rashin sanin muhimmancin su wajen inganta lafiyar su. Wadannan ƙwallaye da kankana ta kunsa suna da arzikin sunadarai da suka hadar da fatty acids, proteins, minerals (magnesium, poatssium, manganese, iron, zinc, phosphorus, copper), vitamin B (thiamine, niacin, folate) da kuma calories.  Bincike ya tabbatar da cewa, ana amfani da ƙwallayen kankana a matsayin abinci a yankunan nahiyyar Asia da kuma wasu yankunan daular Larabawa ta Tsakiya inda ake gasa su kuma kwadanta da ganyayya...

MUSIC : Ali Jita - Mairo Almakura (Giwa)

Wannan wata sabuwa waka ce da ali Jita ya rerawa matar Tanko almakura wanda tayi kyau sosai. Wanda shine munka kawo muku domin saurarenku. DOWNLOAD MP3 Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com