Skip to main content

Rarara ya musunta jita-jitar kona masa shagon wakarsa

Fasihin mawakin siyasa da ke Kano, Dauda Kahutu Rarara ya musanta jita-jitar da ake yadawa cewa an kona shagonsa na daukar wakoki da ke Zoo Road a Kano.
Mawakin ya kuma musanta jita-jitar da ke yawo cewa an kai masa hari don a kashe shi.

Mawakin ya musanta jita-jitar ne a lokacin da ya tattauna ta wayar tarho da wakilin Aminiya a ranar Alhamis da ta gabata.
Ya ce, “Ban san komai a kan batun jita-jitar ba.”

An yada jita-jitar cewa a ranar Talatar makon jiya wadansu ’yan bindiga sun kai wa mawakin hari a shagonsa na daukar waka da ke titin Zoo Road a Kano, inda aka ce Rarara ya tsira amma kuma mahararan sun kona masa shagonsa.
Ya ce, “Wannan zance karya ne, ban san komai a kai ba, Bashir yau ka zo Najeriya ko Kano? Mutane za su yada jita-jitar a kaina saboda wata maunfarsu. Sun taba cewa na yi hadari har an yanke kafafuna da hannuna, sun ce an kona gidana saboda na yi wakar azanci ga Kwankwaso da kuma Shekarau, ina so mutane su sani jita-jita ce babu gaskiya a ciki.”
Mawakin ya ce a yanzu yana cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali.
“Ina cikin halin koshin lafiya da kwanciyar hankali, a yanzu ma ina shagona na daukar waka don yi wa Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje sabuwar waka ta lashe zabe.” Inji Rarara.

Comments

Popular posts from this blog

Kaifin basira da magunguna 4 da kwallon kankana ke yi a jikin dan Adam

Kankana ta kasance daya daga cikin 'ya'yan itatuwa mafi shahara a doron kasa kuma mutane da dama su kan yi santi kwarai yayin kwankwadar ruwanta musamman wadanda kwayoyin halittun su masu bambance dandano ke aiki kwarai. A yayin da kankana ta kasance cikin dangin itatuwa da ake kiransu 'ya'yan duma, 'ƙwallayen cikin da sun ƙunshi sunadarai masu tarin alfanu da kuma tasiri wajen inganta lafiyar jikin dan Adam. Sai dai kash da yawan mutane su kan watsar da ƙwallon kankana a sakamakon rashin sanin muhimmancin su wajen inganta lafiyar su. Wadannan ƙwallaye da kankana ta kunsa suna da arzikin sunadarai da suka hadar da fatty acids, proteins, minerals (magnesium, poatssium, manganese, iron, zinc, phosphorus, copper), vitamin B (thiamine, niacin, folate) da kuma calories.  Bincike ya tabbatar da cewa, ana amfani da ƙwallayen kankana a matsayin abinci a yankunan nahiyyar Asia da kuma wasu yankunan daular Larabawa ta Tsakiya inda ake gasa su kuma kwadanta da ganyayya...

MUSIC : Ali Jita - Mairo Almakura (Giwa)

Wannan wata sabuwa waka ce da ali Jita ya rerawa matar Tanko almakura wanda tayi kyau sosai. Wanda shine munka kawo muku domin saurarenku. DOWNLOAD MP3 Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com