Jagoran APC Bola Ahmed Tinubu ya ce duk wani zababben sanata ko dan majalisar tarayya na APC, tilas ya bi abin da duk jam’iyyar ta gindaya, ko kuma su yi ta zabga masa bulala har sai ya fice daga jam’iyyar.
Tinubu ya ce abin da jam’iyyar APC ta gindaya shi za a bi wajen warware matsalar shugabancin majalisar kasar nan.
Ya furta haka bayan gudanar da addu’o’i da malamai da fastoci suka yi masa jiya Juma’a, a Lagos, domin taya shi murnar cika shekaru 67 a duniya.
“Ya ce yi wa jam’iyya da’a shi ne babban ginshikin jam’iyya. Mun yi sakaci a 2015, muka bada kofa har wani katon kumurci ya shiga cikin jam’iyyar mu, ya hana Najeriya ci gaban da ta yi alwashin samar wa ‘yan kasar nan.
“Kun dai ga yadda muka karke, don haka a wannan karo ba za mu bari irin haka ta sake faruwa ba. Za mu yi da’a ga jam’iyyar mu, kuma za mu sa bulala mu yi ta zabga wa duk wanda ya nemi yi mana kangara.
“Ko dai ka zauna tare da mu, ko ka bi mu sau da kafa, ko kuma ka fice ka bar mu. Ka na da wannan ‘yanci, duk wanda ka zaba ka je ka dauka. Amma ‘yanci bai ce don ba ka da magoya baya sai ka tafi ka farauto magoya baya daga cikin wata jam’iyya, wadda ta yi adawa da mu, kuma ta ke kan adawa da mu ba.
“A wannan karon ba za mu yarda a yi mana sakiyar-da-ba-ruwa ba. Ko kai wane ne, mu haka za mu yi. Shin kai wane ne da har za ka baude ko ka waske daga kan turbar da muka tsara tafiyar da jam’iyyar mu?
Kwanan nan shugabannin APC suka ce sun amince Sanata Ahmed Lawan na Jihar Yobe ne zai zama shugaban Majalisar Dattawa.
Lawan dai na gaban goshin Bola Tinubu ne na gani kashe ni.
Sun kuma amince Hon. Femi Gbajabiamila ne zai shugabanci Majalisar Tarayya.
Nan da nan Sanata Ali Ndume daga Jihar Barno ya ce bai yarda ba, tunda shi ma ya fito takara, sai dai a yi zabe kamar yadda tsarin doka ya tanadar a zauren majalisa.
Ndume ya ce duk wata karfa-karfa, nadi ko dauki dora ba zai tasiri ko karko ba, domin za su kalubalance shi.
Ya ce dauki-dora haramtacciya ce, kuma ba za su amince da ita ba.
Baya ga Ndume, Sanata Danjuma Goje ma ya na neman kujerar ta shugabancin majalisar dattawa.
APCke da mafi rinjaye a majalisar dattawa, inda ta ke da 60 daga cikin 109.
Idan ba a manta ba, bayan zaben 2015, APC ta nemi dora Lawan da Gbajabiamila a matsayin shugaban dattawa da shugaban majalisar tarayya, amma aka yi wa jam’iyyar tawaye, aka zabi Saraki da Yakubu Dogara.
Comments
Post a Comment