Kadan daga cikin abubuwan dake sanya Kauna, Farinjini da Kwarjini, bugu da kari kuma ayyukan lada ne da suka dace da sunnan Annabi (SAW):
1) Yin fara’a, sakin fuska da murmushi ga mutane tare da Sallama a garesu
2) Kiran mutane da mafi soyuwan sunayen su, tare da girmamawa cikin salon murya mai dadi.
3) Girmama na gaba da kimanta na kasa tare da nisantar wulakaci ko tozarci agare su acikin mu’amala ko Magana.
4) Tsafta da cikakken tsare a cikin sutura, abinci, da duk wata mu’amala da mutum ya keyi a rayuwarsa.
5) Yin Ado da kwalliya tare da kamshi da shiga ta kamala.
6) Nuna farinciki yayin farincikin mutane, da damuwa acikin damuwarsu tare da bada gudun muwa a cikin rayuwarsu.
7) Gaskiya da rikon amana, tare da taimokon gaskiya ta masu gaskiyar.
8) Kyauta da kawaici, tare da kauda kai da rashin kwadayi.
9) Taimako ga mabukata da rashin hasada ga wadanda Allah ya yi wa daukaka.
10)Adalci da girmama mutane.
11)Hakuri da dogaro ga Allah tare da rashin hadama.
12)Rashim girman kai.
13)Karban gyara da nasiha idan mutum yayi kuskure.
14)Jin tsoron Allah da kyauta ibada tare da tsare dokokin Allah.
A karshe, ba zaka iya samun kauna da soyayyan kowa da kowa ba, amma kuma zaka iya canza tsarin rayuwarka ta hanyar kyatata halayenka da dabi’unka har Allah ya soka kuma ka samu kauna daga mafi yawan al’uma.
Abisani kuma farinjininka da kwarjininka ya karu a wajen Al’uma.
Allah ka rabamu da Kaikasasshen Talauci ka Wadatamu da Wadatar Zuci. Amin
Comments
Post a Comment