A yanzu haka rundunar Yansandan Najeriya na farautar fitacciyar jarumar fina finan Kannywood, Ummi Zee Zee sakamakon kararta da shahararren jarumin Kannywood Zaharaddeen Sani ya shigar da ita saboda tuhumarta da yake da bata masa suna. Jaridar Premium Times ta ruwaito makasudin wannan rikici shine Zee Zee ta zargi wasu yan fim da suka hada da Zaharaddeen, Sani Danja, Yakubu Muhammed, Al’Ameen Buhari, Fati Mohammed, da Imarana Mohammed da wareta a lokacin da suka gana da wakilan Atiku Abubakar a Kaduna.
Zaharadden Sani ya bayyana cewa Zee Zee bata da masaniya game da taron, su suka shirya abinsu ba tare da sun sanyata ciki ba, kuma sun bayyana ma wakilan Atiku Abubakar irin gudunmuwar da suke bashi a matsayinsu na taurarin Kannywood. A lokacin da Zee Zee ta samu labarin taron, sai ta nemi abokanan aikinta dasu bata nata Kason alherin da suka samo daga taron, wanda jagoran yakin neman zaben Atiku, shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Sarakiya halarta. Kammala wannan taro keda wuya sai Zee Zee ta buga a shafinta na Instagram tana zargin su Zaharaddeen da yaudaranta, tana kiransu barayi, har ma ta yi barazanar dauresu dukansu, inda take bugun kirji cewa duk ta fisu sanin manya a Najeriya. “Ina da labarin Atiku ya aiko mana da makudan kudade, amma da yake ku barayi ne sai kuka rabe kudin a tsakaninku, wallahi da ba don mahaifiyata ta bani hakuri ba, da sai na daureku gaba daya, sai gashi bayan taron Zaharaddeen ya aiko min da N25,000, kai ka sani ni fa mabaraciya bace, daga yau sai yau, idan kuka sake min irin haka sai na yi maganinku.” Inji ta.
Sai dai Zaharadden ya tabbatar ma majiyar Legit.ng cewa N25,000 daya baiwa Zee Zee kyauta ne daga aljihunsa, saboda a cewarsa bada ita suka shirya taron ba, kuma bata da wata gudunmuwa da zata basu saboda bata da sauran tasiri a Kannywood. “Ina so ka sani cewa a yanzu haka na shigar da kararta gaban hukumar Yansanda a Kaduna, kuma tuni suka shiga nemanta ruwa a jallo, na kai kararta ne saboda ta zargeni da abokanaina da tafka laifin sata, wai mun kwashe kudin da Atiku ya bamu” Inji shi. Zuwa yanzu ta bayyana cewa akwai magoya bayan takarar shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma akwai masu goyon bayan Atiku Abubakar, wasu daga cikin magoya bayan Buhari sun hada da Ali Nuhu, A Zango, Rabiu Rikadawa, da sauransu.
Comments
Post a Comment