Wole Soyinka, kwararre kuma sanannen marubuci yace ba zai goyi bayan yan takara biyun ba na fitattun jam’iyyun siyasar da suka fito takarar shugabancin kasa. Yace hakan ne a zauren tattaunawa na yan kasa a na 2019. “Lokaci ne yanzu na sabuwar alkibla kuma idan wani dan takara ya bayyana zamu bashi goyon baya,” a cewar shi. Shugaban kasa Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP sune yan takara biyu dake kan gaba. Soyinka yace ” yanzu lokaci ne na canza alkiblar kasar nan ta hanyar da ya dace. “Don gujewa tantama, bari in fadi matsayata saboda bana son in zama mai harshen damo; “Ni Wole Soyinka bazan zabi kowa daga cikin sanannun ‘yan takarar biyu ba. Na gano cewa dukkanin su basu cancanci kuri’a ta ba,” inji shi. “A saboda dalilai na wadanda ba sai na bayyana ba, banda ra’ayin su. Matsayata mai sauki ce, itace lokaci yayi da zamu canza alkibla. Kuma kiri kiri ba ni kadai bane, akwai wata kungiya dake taro a Legas don fi...