Skip to main content

MACE SAI DA GYARA: Abubuwa 12 Wadanda Duk Matar Da Ta Rike Su Za Ta Samu Alkhairi A Rayuwarta Ta aure


1 - Ki Zama Kamar Baiwa Ga Mijinki, Sai Shi
Ma Ya Zama Kamar Bawa A Gare Ki.

1 - Kada Ki Nisance Shi; Sai Ya Manta Da ke.

3 - Ki Kiyaye Masa Hancinsa, Jinsa, Da
Ganinsa; Kada Ya Shaqi Wani Abu Daga Gare
Ki Sai Mai Kamshi, Kada Ya Ji Wani Abu Daga
Bakinki Sai Mai Dadi, Kada Ya Ga Wani Abu
Daga Gare Ki Sai Mai Kyau.

4 - Ki Kiyaye Masa Lokacin Abincinsa Da
Lokacin Baccinsa, Domin Yunwa Tana
Hassala Mutum, Kuma Ta Gurbata Masa Bacci
Ta Fusata Shi.

5 – Ki Kiyaye Masa Dukiyarsa, Danginsa Da
Gidansa, Domin Suna Da Matukar
Muhimmanci A Gare Shi.

6 - Ki Guji Yin Farin Ciki Yayin Da Yake Cikin
Bacin Rai, Kuma Ki Kiyayi Yin Bakin Ciki, Yayin
Da Yake Farin Ciki.

7 - Ki Girmama Shi Matuka; Shi Ma Zai
Girmamaki Matuka Fiye Da Yadda Kowa Zai
Girmamaki.

8 - Ki Sani Cewa Gwargwadon Yadda Kike
Amincewa Da Ra’ayinsa Gwargwadon
Tausayawar Da Zai Miki.

9 - Kada Ki Juya Masa Baya Yayin Da Ya
Kusanto Gare Ki.

10 - Ki Sani Baza Ki Sami Yadda Kike So Ba
Har Sai Kin Zabi Yardarsa Akan Yardarki, Kin
Fifita Son Ransa Akan Son Ranki.

11 - Kada Ki Fiya Naci Ko Fushi A Lokacin Da
Kike Neman Wani Abu A Gare Shi, Sai Ya Kosa
Dake.

12 - Daga Karshe Don Girman ALLAH Ki Yi
Hakuri, Ki Zamo Shimfida Ga Mijinki Zai Zamo
Rumfa A Gare Ki.

Comments

Popular posts from this blog

Kaifin basira da magunguna 4 da kwallon kankana ke yi a jikin dan Adam

Kankana ta kasance daya daga cikin 'ya'yan itatuwa mafi shahara a doron kasa kuma mutane da dama su kan yi santi kwarai yayin kwankwadar ruwanta musamman wadanda kwayoyin halittun su masu bambance dandano ke aiki kwarai. A yayin da kankana ta kasance cikin dangin itatuwa da ake kiransu 'ya'yan duma, 'ƙwallayen cikin da sun ƙunshi sunadarai masu tarin alfanu da kuma tasiri wajen inganta lafiyar jikin dan Adam. Sai dai kash da yawan mutane su kan watsar da ƙwallon kankana a sakamakon rashin sanin muhimmancin su wajen inganta lafiyar su. Wadannan ƙwallaye da kankana ta kunsa suna da arzikin sunadarai da suka hadar da fatty acids, proteins, minerals (magnesium, poatssium, manganese, iron, zinc, phosphorus, copper), vitamin B (thiamine, niacin, folate) da kuma calories.  Bincike ya tabbatar da cewa, ana amfani da ƙwallayen kankana a matsayin abinci a yankunan nahiyyar Asia da kuma wasu yankunan daular Larabawa ta Tsakiya inda ake gasa su kuma kwadanta da ganyayya...

MUSIC : Ali Jita - Mairo Almakura (Giwa)

Wannan wata sabuwa waka ce da ali Jita ya rerawa matar Tanko almakura wanda tayi kyau sosai. Wanda shine munka kawo muku domin saurarenku. DOWNLOAD MP3 Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com