Jennifer Gate, diyar hamshakin mai kudin nan na duniya za ta angwance da masoyinta dan asalin kasar Egypt - Masoyan junan sun dau a kalla shekaru hudu suna soyayya kafin daga bisani sun yanke shawarar auren juna - Nasel Nassar dai babban miloniya ne dan asalin kasar Egypt amma mazaunin kasar Kuwait ne Diyar Bill Gate, Jennifer Gates za ta angwance nan ba da dadewa ba bayan an sa ranar aurenta da masoyinta dan asalin kasar Egypt mai suna Nayel Nassar, kamar yadda jaridar Gistmania ta ruwaito. Jennifer da Nassar sun dau a kalla shekaru hudu suna soyayya kafin daga baya ya bayyana bukatar aurenta. Masoyan junan kan yi tafiye-tafiye tare, kuma su na wallafa hotunansu a kafar sada zumuntar zamani ta Instagram. An yiwa 'yar gidan mai kudin duniya Bill Gates baiko da Musulmi dan Afrika Jennifer mai shekaru 23 a duniya ta sanar da sa ranarta tare da hamshakin miloniya dan kasar Egypt. Ta rubuta: " Nayel Nassar, kai daya ne tamkar da goma. Gaskiya ka shayar dani mamaki...